Yan bindiga dauke da muggan makamai cikin shigar mata, sun Kai hari kauyen Mallamawar Yari da ke karamar hukumar Rabah a jihar sakkwato.
Yayin harin, ‘yan bindigar sun kashe mutanen kauyen da dama tare da garkuwa da wasu.
Mai sharhi kan al’amuran tsaro Rahoton, Bakatsine ya tabbatar da kai harin a wata sanarwa a shafinsa na X.
Bakatsine ya ce, ‘yanbindigar sun yi wa kauyen dirar mikiya ne a daren jiya lahadi wayewar garin yau litinin, sanye da hijabai da shiga irin ta mata, wanda hakan ya ba su damar shiga lungu da sakon garin ba tare da wani ya zargesu ba.
Zuwa yanzu babu cikakkun alkaluma na wadanda suka rasu yayin harin, sannan babu masaniya kan inda aka kai wadanda aka yi garkuwa da su.
Wannan lamari dai ya jefa shakku da tsoro cikin zukatan mazauna yankin, inda harin yan bindiga ke ci gaba da mamaye sassan jihar Sokoto.