Gwamna jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanar da ficewa daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar APC mai mulki.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Nuhu Salihu Anka ya fitar, inda ya ce ya yanke shawarar ce bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da magoya bayansa.
Gwamnan ya ce rikice-rikicen da suka dabaibaye jam’iyyar PDPn a kowanne mataki kama daga tarayya zuwa sauran rassanta dake jihohi na cikin dalilai da suka da ya dauki matakin sauya sheka.
Sanarwar ta kara da cewa, komawarsa jam’iyya mai mulki ne zai ba shi dama wajen ci gaba da yi wa al’ummar Zamfara ayyuka nagari.
Kazalika sanarwar ta kara da cewa babban fatansa shi ne, samun zaman lafiya da tsaro don ci gaban jihar Zamfara.