Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Amurka ta gargadi ‘yan kasarta kan kai hari Najeriya

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce akwai yiwuwar a kai harin ta’addanci kan ofishin jakadancinta da makarantunta da ke kasar.

Ofishin jakadancin ya shawarci ‘yan ƙasar su riƙa sauya hanyoyi da lokutan tafiye-tafiye da kuma kauce wa tafiyar da rayuwarsu ta yadda za a iya hasashen abin da za su yi nan gaba tare da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana.

Wannan gargadi na zuwa ne yayin da yaƙi tsakanin Amurka-Isra’ila da Iran ke ci gaba da tsananta cikin kasa da mako biyu da fara yakin.

Sauran shawarwarin da Amurkar ta bai wa ‘yan kasarta a Najeriya sun haɗa da tabbatar da cewa wayoyin salularsu na da cikakken caji domin ko-ta-kwana da kuma sanin hanyoyin ficewa cikin gaggawa kafin su shiga ko wane gini.

Sai dai hukumomi sun ce duk da haka ofisoshin jakadancin za su ci gaba da aiki.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use