Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich na shirin daukar mataki mai girma a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa, inda ake rade-radin cewa tana son daukar dan wasan Najeriya Victor Osimhen domin maye gurbin tauraron Ingila Harry Kane.
Rahotanni sun bayyana cewa kulob din ya riga ya yi tayin kusan yuro miliyan 115 ga Galatasaray domin dauko dan wasan.
Rahotanni sun nuna cewa akwai yiwuwar Kane ya bar kungiyar ko kuma Bayern na son fara shirye-shirye na gaba saboda shekarunsa sun fara ja.
Don haka kulob din yana neman sabon dan wasan gaba wanda zai jagoranci kungiyar nan gaba.
A cewar wasu rahotanni daga Turkiyya, tsohon dan wasan Besiktas Sinan Engin ne ya bayyana cewa Bayern ta nuna matukar sha’awa ga Osimhen kuma ta yi tayin kudi mai yawa domin daukarsa.
Victor Osimhen yana taka rawa sosai a kungiyar Galatasaray, kuma magoya bayan kungiyar na ganin darajarsa ta wuce auna da kudi.
Dan asalin Najeriyar mai shekaru 27 yana cikin kyakkyawan yanayi, inda ya zura kwallaye da dama tare da taimakawa kungiyar a gasa daban-daban.
Wannan ne ya sa manyan kungiyoyi a Turai ke nuna sha’awa a kansa.