Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Za a daure mai shiga jam’iyyu biyu a lokaci guda – Majalisar Wakilan Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da daure duk wanda aka samu da laifin shiga jam‘iyyun siyasa biyu a lokaci guda.


Majalisar ta sanar da matakin ne bayan yi wa dokar zabe ta shekarar 2026 gyaran fuska domin dakile matsalar.


Hukuncin ya tanadi cewa duk wanda aka kama yana da rajista a jam’iyyun siyasa fiye da daya a lokaci guda zai iya fuskantar tara ta naira miliyan 10, ko daurin kurkuku na tsawon shekaru biyu, ko kuma duka biyun tare.

Majalisar ta bayyana cewa an yi wannan gyara ne domin karfafa tsarin dimokuradiyya a Najeriya tare da tabbatar da cewa dokokin jam’iyyun siyasa suna aiki yadda ya kamata.


Ana sa ran cewa idan aka kammala dukkan matakan da suka rage na doka, wannan gyara zai taimaka wajen tsaftace harkokin siyasa da kuma tabbatar da gaskiya a tsarin jam’iyyun siyasa a Najeriya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use