Hukumar kare hakkin masu saye da amfani da kayayyaki a Najeriya (FCCPC) ta ce tana nazarin yiwuwar ɗaukar mataki kan wasu kamfanonin jiragen sama na cikin gida guda biyar bisa zargin haɗa baki wajen kara farashin tikitin jirgi a lokacin bukukuwan Kirsimeti na shekarar 2025.
Hukumar ta ce ta fara binciken ne bayan korafe-korafen matafiya da suka ce farashin tikitin jirgi ya yi tashin gwauron zabi a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
A cewar wani jami’in hukumar, Babatunde Irukera Bello, binciken farko ya nuna alamun yiwuwar haɗin baki tsakanin wasu kamfanonin jiragen sama wajen ƙara farashin tikiti a lokaci guda.
Ya ce farashin tikiti da a baya ke kaiwa tsakanin naira 45,000 zuwa 50,000 ya haura zuwa tsakanin naira 400,000 da 670,000 a wasu lokuta na lokacin bukukuwa.
Hukumar ta ce tana kuma nazarin yiwuwar tilasta wa kamfanonin da ake zargi su mayar wa wasu matafiya kuɗaɗen da suka biya fiye da kima idan binciken ƙarshe ya tabbatar da cewa an karya dokokin kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki da ayyuka.