Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Yan sanda sun kama mutane biyu kan sace yaro mai shekara huɗu a Adamawa

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu

Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da sace wani yaro mai shekara huɗu a ƙauyen Ngballang da ke ƙaramar hukumar Numan ta jihar.

Rundunar ta ce wani mai suna Umar Ibrahim, mazaunin Ngballang, ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda a Numan ranar 2 ga Maris 2026 cewa a ranar 1 ga watan Maris ɗansa mai shekara huɗu mai suna Ramadan ya fita wasa amma bai dawo gida ba.

A cewar rundunar, bayan wasu kwanaki sai mahaifin yaron ya samu kiran waya daga wata baƙuwar lamba, inda aka sanar da shi cewa an sace yaron, tare da neman kudin fansa na naira 800,000 domin a sake shi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar, Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce binciken da jami’an rundunar da ke karamar hukumar Numan suka gudanar ya kai ga kama wasu mutane biyu duk mazauna Lafiya a ƙaramar hukumar Lamurde da ake zargi da sace yaron.

Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin Sadiq Ali mai shekara 19, da Shitu Umar mai shekara 23, sun amsa laifin aikata satar yaron yayin tambayoyi, kuma an mika lamarin ga sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan da suka dace.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use