Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Gwamnatin Najeriya ta ayyana Alhamis da Juma’a hutu don murnar bikin karamar Sallah

Ministan cikin gida na Najeriya, Olabunmi Tunji Ojo

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Alhamis 19 da kuma Juma’a 20 ga watan Maris a matsayin hutu don shagulgulan bikin Sallah.

Wata sanarwa da ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya fitar, ya taya al’ummar Musulmi murna tare da fatan yin bukukuwa lafiya.

Ya bukaci Musulmi da su dabbaka zaman lafiya, kauna da kuma sadaukarwa da suka koya lokacin azumi.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use