Wasu ma’aikatan lafiya da marasa lafiya sun jikkata sakamakon wani harin sama da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Sanarwar da Asibitin Jami’ar Sheikh Ragheb Harb da ke Toul, kusa da garin Nabatieh, ta fitar ta ce harin ya lalata wasu muhimman sassa na asibitin, ciki har da sashen kula da marasa lafiya masu matsanancin hali (ICU).
Rahotanni sun nuna cewa jikkatar ta faru ne sakamakon shaƙar hayaki bayan harin ya auka kan wani gini da ke makwabtaka da asibitin.
Mahukuntan asibitin sun bayyana harin a matsayin take dokokin ƙasa da ƙasa, tare da cewa ya jefa rayuwar marasa lafiya da ma’aikatan lafiya cikin haɗari.