Wata matatar mai ta Isra’ila da ke birnin Haifa ta samu tawaya bayan harin makamai masu linzami da Iran ta kai.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya jawo tsaiko a matatar, tare da katsewar wutar lantarki na wucin gadi, amma ba a samu asarar rayuka ba.
Hukumomin Isra’ila sun ce sun samu nasarar dakile wasu daga cikin makaman kafin su kai ga sauka.
Ana ganin harin na da alaƙa da rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin Iran da Isra’ila, inda kowanne ɓangare ke kai hare-hare kan muhimman wuraren makamashi.
Masana sun yi gargaɗin cewa wannan rikici na iya ƙara tayar da hankali a yankin Gabas ta tsakiya tare da shafar farashin mai a kasuwannin duniya.