Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Atiku, Obi da Amaechi ba su da sabon tsari na kada Tinubu a 2027’ – Ndume

Sanata Ali Ndume, dan majalisan dattawan Najeriya mai wakiltan Borno ta kudu

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa manyan ‘yan adawa Atiku Abubakar, Peter Obi da Rotimi Amaechi ba su kawo wani sabon tsari da zai iya kayar da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ba.

Ya ce jam’iyyar APC na da damar ci gaba da mulki, musamman idan gwamnati ta inganta tsaro da rayuwar jama’a.

Duk da haka, Ndume ya ce bai kamata a raina ‘yan adawa ba, domin za su iya sauya akalar siyasa idan suka samu haɗin kai da ingantaccen tsari.

Ndume ya jaddada cewa makomar zaɓen 2027 za ta fi karkata ga yadda gwamnati za ta magance matsalolin ƙasa, ba wai sunayen ‘yan takara kaɗai ba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use