Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Amurka da Isra’ila sun sake kai hari cibiyar nukiliyar Natanz a Iran

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa Amurka da Isra’ila sun kai hari cibiyar nukiliya ta Natanz a safiyar yau.

Rahoton ya bayyana cewa harin ya shafi wani ɓangare na cibiyar da ke da muhimmanci wajen shirin nukiliyar Iran, lamarin da ya ƙara tayar da hankali a yankin.

Sai dai kamfanin ya tabbatar da cewa ba a samu yoyo ko zubar sinadarin radiation sakamakon harin ba.

Haka kuma, an ce babu wata barazana ga mazauna yankunan da ke kewaye da cibiyar duk da harin da aka kai.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use