Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Ba ma neman rikici da makwabtanmu – Iran

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce ƙasarsa ba ta neman rikici da ƙasashen makwabta na yankin Gulf da sauran ƙasashen Musulmi, inda ya bayyana su a matsayin “’yan’uwa”.

Ya ce: “Ga ƙasashen Musulmi da makwabtanmu masu daraja, ku ’yan’uwanmu ne, kuma ba mu cikin wani rikici da ku. Wadda kawai ke cin gajiyar rashin jituwarmu ita ce Isra’ila.”

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.

Ya kuma yi addu’ar cewa wannan sallar (Eid al-Fitr) za ta ƙarfafa haɗin kai ta hanyar bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), sannan ya yi maraba da sabuwar shekarar Iran.

Ya ce: “A wannan shekara fiye da kowane lokaci, muna buƙatar sabuwar shekarar farisawa (Nowruz) ta kasance mai cike da haɗin kai, jituwa da kuma haɗin kan ƙasa a al’adunmu. Mu haɗa hannu don jagorantar Iran ta fuskanci ƙalubalen da take ciki, domin ta fito cikin alfahari da nasara.”

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use