Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce hare-haren Iran na baya-bayan nan sun nuna cewa ƙasar na barazana ga duniya baki ɗaya, yana mai cewa an kai hari kan yankunan farar hula duk da cewa babu wanda ya mutu.
Ya ƙara da cewa Iran ta kuma harba makamai kusa da wuraren ibada masu muhimmanci a birnin Jerussalam, ciki har da wasu majami’u da masallacin Al-Aqsa, yana mai cewa hakan na nuna haɗari mai girma.
Netanyahu ya ce Iran ta kuma harba makami mai linzami mai nisan kusan kilomita 4,000, wanda ke nuna cewa tana da ikon kai hari har cikin Turai, tare da zargin ta da hana zirga-zirgar jiragen ruwa da hanyoyin makamashi na duniya.
Da yake tattaunawa da manema labarai bayan sabbin hare-haren da Iran ta kaddamar kan kasarsa, Netanyahu ya ce Isra’ila da Amurka na aiki tare domin dakile wannan barazana, yana mai kira ga sauran ƙasashen duniya su haɗa kai domin tinkarar Iran.
A bangaren martani, ya ce Isra’ila na kai munanan hare-hare amma ba kan farar hula ba, yana mai cewa suna kai hari kan shugabannin Iran, rundunar IRGC da kuma cibiyoyin tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa manyan manufofin Isra’ila sun haɗa da rusa shirin nukiliya da na makamai masu linzami na Iran gaba ɗaya, tare da samar da yanayin da zai bai wa al’ummar Iran damar kifar da gwamnatin da yake zargi da zalunci.