Shugaban Hukumar Kula da Makamin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya bayyana cewa yana fatan a sake farfado da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirin nukiliyar Iran.
Ya shaida wa manema labarai a Amurka cewa yana gudanar da muhimman tattaunawa a Fadar White House, da kuma ɓangaren Iran kan lamarin.
Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar cimma yarjejeniya, Grossi ya ce duk inda ake tattaunawa, akwai damar cimma matsaya.
Ya kuma bayyana cewa ko da bai yi magana kai tsaye da Shugaba Donald Trump ba, yana sane da cewa shugaban na goyon bayan diflomasiyya.