Jami’ar Bayero Kano ta amince da korar dalibai 171 bayan samunsu da laifin gabatar da takardun ƙarya domin samun gurbin karatu.
An cimma wannan matsaya ne a zaman majalisar gudanarwar jami’ar karo na 433 da aka gudanar a ranar 4 ga watan Maris, 2026, bayan wani bincike da Kwamitin Majalisar kan matsalolin sahihancin takardun shiga ya gudanar.
A wata sanarwa da jami’ar ta wallafa a mujallar ta na mako-mako a ranar Juma’a, ta bayyana cewa an gano daliban sun gabatar da takardun bogi ne a lokacin da suke neman shiga jami’ar.
Jami’ar ta ƙara da cewa wannan laifi ya saɓa da sashe na 20.7, rukuni na A na dokokinta da suka shafi jarabawa da harkokin karatu, wanda ke tanadar da hukuncin kora ga duk wanda aka samu da irin wannan laifi.
Haka kuma, jami’ar ta bayyana cewa daliban da abin ya shafa sun fito daga sassa daban-daban da kuma matakai mabanbanta, tana mai cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin tsaftace tsarin karatu da bayanan dalibai na jami’ar.