Rasha ta nuna damuwa kan hare-haren Amurka da Isra’ila a kusa da tashar nukiliya ta Bushehr a Iran, inda mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce hakan zai haifar da sakamako mara kyau.
“Mun yi imanin cewa hari kan tashoshin nukiliya na da babbar barazana… don haka, muna daukar wasu matakai a bangaren mu, kuma mun sha nuna damuwa kan lamarin, in ji Peskov.
Ya ce ya kamata a mayar da hankali kan tattaunawar diflomasiyya wajen warware rikicin Iran.
“Wannan ita ce hanya kadai da za ta iya yayyafawa rikicin ruwa ganin yanzu matsalar ta girma zuwa fadin yankin.”