Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Trump ya yi ikirarin tattaunawa mai ma’ana da Iran kan kawo karshen yaki

Trump Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce gwamnatinsa ta yi wata tattaunawa mai ma’ana da Iran kan bukatar tsagaita wuta gaba daya a yankin Gabas ta Tsakiya a cikin kwanaki biyu da suka gabata.

“Za mu ci gaba da yin irin wannan tattaunawa har zuwa karshen wannan mako, na umarci sashen kula da harkokin yaki cewa ya janye duk wani hari da ake shirin kai wa tashoshin nukiliyar Iran da kuma cibiyoyin makamashi na tsawon kwanaki biyar, don duba irin nasarar da za a samu a tattaunawar,” in ji Trump a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

Amurka-Isra’ila da Iran dai na ci gaba da kai wa juna hare-hare babu kakkautawa a daidai lokacin da yakin ke shiga mako na uku da fara wa.

Masana dai na gargadin cewa muddin ba a tsagaita wuta ba, tasirin da rikicin zai yi a duniya zai zama mai munin gaske.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use