Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Kotu ta dage shari’ar El-Rufai zuwa 31 ga watan Maris

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kaduna ta ɗage sauraron buƙatar beli da tsohon gwamnan jihar, Nasir El‑Rufai ya gabatar, inda ta ce za ta yanke hukunci a ranar 31 ga watan Maris.

An ɗage shari’ar ne bayan zaman kotun a yau Talata, inda lauyoyin ɓangarorin biyu suka gabatar da hujjojinsu kan ko ya dace a ba shi beli ko a’a.

A zaman na yau, lauyan El-Rufai ya roƙi kotu ta ba shi beli, yana mai cewa hakan na daga cikin haƙƙinsa na doka, tare da buƙatar samun damar shirya kare kansa yadda ya kamata.

Sai dai ɓangaren masu gabatar da ƙara sun yi adawa da hakan, suna cewa tuhume-tuhumen da ake masa masu tsanani ne, kuma bayar da beli na iya kawo cikas ga binciken da ake ci gaba da yi.

Rahotanni sun ce har yanzu tsohon gwamnan na ci gaba da kasancewa a tsare, yayin da ake jiran hukuncin kotu kan batun belin nasa a ƙarshen watan nan.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use