Dakarun rundunar sojin Najeriya ta 29 Brigade karkashin aikin Operation HADIN KAI, tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force (CJTF), sun kama wani mutum da ake zargi da daukar mutane zuwa kungiyar Boko Haram a garin Benesheikh na jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun ce an gano wanda ake zargin ne ta hanyar sahihan bayanan sirri da suka danganta shi da ayyukan janyo mutane shiga kungiyar ta’addanci.
An kama shi ranar 24 ga Maris yayin wani samame na hadin gwiwa a yankin, kuma a halin yanzu yana hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike.