Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Yadda DSS ta hana matan El-Rufai shiga kotun da aka gurfanar da mijin su

Matan tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i da suka hada da Asiya Ahmed El-Rufa’i da Khadija Ahmed El-Rufa’i sun samu tsaiko a kofar shiga kotun da aka gurfanar da mijin su yau a jihar Kaduna, don fuskantar tuhume-tuhumen da hukumomin ICPC da EFCC ke masa.

Tun da farko, Asiya da ke a matsayin amaryar tsohon gwamnan ta bayyana a harabar kotun a fusace tare da kokarin shiga kotun inda mijin nata yake, sai dai jami’in DSS da ke bakin kofar ya hanata shiga, inda ta rika maganganu, wanda a karshe jam’in ya nuna mata wata kofa ta baya don ta shiga.

Lokuta kadan ita ma uwar gidan El-Rufa’i, Khadija Ahmed El-Rufa’i ta isa harabar kotun tare da kokarin shiga, sai dai ita ba ta yi hayaniya ba, aka nuna mata kofar baya ta shiga.

Ko daya ke an jiyo amaryar tsohon gwamnan na fadin ‘Duk abin da ake yi mana a yanzu zai wuce, wata rana sai labari’, Asiya ta furta haka ne sa’ilin da take fada wa jam’in DSS da ya hana ta shiga kofar da aka shigar da mijin ta kotu maganganu.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use