Hare-haren da sojojin Amurka da na Isra’ila suka kai Iran, sun lalata gine-ginen fararen hula sama da 82,000, in ji kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran.
Gidajen da suka lalace sun hada da gidaje 62,000, cibiyoyin kiwon lafiya 281 da shagunan sayar da magani.
Bugu da kari, an lalata makarantu 498 da kuma wuraren agaji 17 da motocin ceto 12.