Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Fitaccen malami Sheikh Ahmad Tijjani ya musanta batun cafke shi

Fitaccen malamin addini a jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Tijjani Umar ya yi watsi da batun kama shi da ake ta yaya ta wa.

Hakan na zuwa ne bayan kalaman tsohon dan takarar shugaban kasa a jama’iyyar Labour, Peter Obi, ya yi na cewa hukumar DSS ta cafke malamin a safiyar yau Talata, kan gayyatar da malamin ya yi masa zuwa gidansa da ke jihar Kaduna a ranar Lahadi.

Sheikh Ahmad Tijjani ya ce babu wani jami’in DSS da ya kama shi ko ya tuhumeshi kan zuwan Obi gidansa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use