Tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya ce Najeriya na cikin matsala mai tsanani fiye da lokacin da shugaba Tinubu ya karɓi mulki a 2023, yana mai danganta hakan da ƙaruwar matsalar tsaro da na rayuwa.
Baba-Ahmed ya bayyana cewa bayan kusan shekaru uku na mulkin Tinubu, hare-haren ta’addanci da tasirinsu sun ƙaru sosai, inda ya ce irin wannan yanayi bai taba kai wannan mataki ba a baya.
Ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi da manema labarai, inda ya jaddada cewa gwamnati ta gaza cika alkawurran da ta ɗauka na kawo ƙarshen rashin tsaro da inganta rayuwar al’umma.
A cewarsa, Tinubu ya hau mulki ne da alkawarin samar da tsaro da walwala ga ‘yan Najeriya, amma har yanzu mutane na fuskantar matsaloli masu tsanani, musamman a fannin tsaro da tattalin arziki.
Baba-Ahmed ya kuma soki ziyarar da shugaban ya kai Birtaniya kwanan nan, inda ya ce ta zo ne a lokacin da ake fuskantar munanan hare-hare a cikin ƙasar – ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa don shawo kan matsalolin da ke ƙara ta’azzara.