Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa za ta rufe dukkan cibiyoyin Almajirai da ba su cika sabbin ƙa’idojin da aka kafa ba a faɗin ƙasar.
Ma’aikatar Ilimi ta tarayya ta bayyana cewa wannan mataki na cikin sabuwar manufar inganta ilimin Almajirai, wadda ke da nufin kawo tsari, da kuma kare haƙƙin yara.
Sabbin ƙa’idojin sun haɗa da wajabta yin rijista da gwamnati, haramta bara ga ɗalibai, da kuma tabbatar da kulawar lafiya da ingantaccen muhalli a makarantu.
Gwamnati ta bai wa cibiyoyin wa’adin watanni uku zuwa shida su gyara kura-kuransu, inda ta ce duk wanda ya gaza zai fuskanci rufe wa.
Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da sa ido domin tabbatar da cewa tsarin Almajirai ya dace da zamani tare da kare martabar yara.