Sojoji sun samu nasarar kwantar da tarzoma bayan wani rikici da ya barke a kasuwar Iware da ke ƙaramar hukumar Ardo-Kola a Jihar Taraba, wanda ya haddasa tashin hankali a yankin.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun kai ɗauki cikin gaggawa, inda suka dakile rikicin tare da dawo da zaman lafiya. Bayan haka, an ƙarfafa tsaro a yankin domin hana sake barkewar rikici.
Hukumomi sun yi kira ga al’umma da su kiyaye doka da oda tare da ba jami’an tsaro haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.