Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Rundunar IRGC ta ƙaddamar hare-hare kan kamfanonin Bahrain da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

Aluminium Facility in Bahrain

Rundunar juyin-juya halin Iran ta ce ta ƙaddamar da hare-haren makami mai linzami da kuma jirage marasa matuka a wuraren aikin aluminium a Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

A wata sanarwa da gidan talabijin na gwamnati na Iran IRIB ya fitar daren Lahadi, IRGC ta ce wuraren da aka kai harin a ranar Asabar suna da alaka da rundunar sojin Amurka.

Kamfanin Aluminium Bahrain (Alba) ya ce harin ya raunata ma’aikata biyu, yayin da kamfanin Emirates Global Aluminium (EGA) na UAE ya tabbatar da lalacewar daya daga cikin wurarensa a Abu Dhabi inda mutane shida suka ji rauni.

IRGC ta ce harin da suka kai martani ne ga harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan masana’antar Iran, wanda aka kaddamar daga sansanonin soji da ke dauke da dakarun Amurka a kasashen Gulf.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use