Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Dakarunmu suna jiran zuwan sojojin Amurka ta ƙasa don buɗe musu wuta — Iran

Mohammad Bagher Ghalibaf - Kakakin Majalisar Dokokin Iran

Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce rundunar sojin Iran ta shirya don zuwan dakarun Amurka.

A wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na IRNA ya wallafa, Ghalibaf ya soki Trump saboda nuna sha’awar tattaunawa da Iran a fili, yayin da a ɓoye yake shirin kai farmaki ta ƙasa.

“Ina ganin abokin gaba a fili yana magana kan tattaunawa, amma a ɓoye yana shirin kai farmaki ta ƙasa. Mutanenmu suna jiran zuwan sojojin Amurka a ƙasa don buɗe musu wuta,” in ji shi.

Kafofin labarai na Amurka sun ruwaito cewa Pentagon na shirin ƙaddamar da ayyukan soji ta ƙasa a Iran na tsawon makonni, bayan rundunar sojin Amurka ta sanar da isowar sojoji 3,500 zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use