Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Syria ta daƙile harin jirage marasa matuƙa daga Iraki kan sansanin sojin Amurka

Sojojin Syria sun daƙile harin jirage marasa matuƙa da aka kai daga Iraki kan ɗaya daga cikin ƙananan sansanonin sojin Amurka da suka rage a ƙasar, a cewar wani babban jami’i.

“Yau da safe, an kai hari kan sansanin Amurka a Qasrak, wanda ke cikin ƙasarmu, ta hanyar jiragen marasa matuka huɗu da aka harba daga ƙasar Iraki,” in ji Mataimakin Ministan Tsaro, Sipan Hemo, a shafin X, yana mai ƙarawa da cewa “an harbe jiragen ba tare da raunata kowa ba.”

Ya ƙara da cewa “mun ɗora alhakin hakan kan Iraki kuma muna kira gare ta da ta hana sake faruwar hare-hare da ke barazana ga zaman lafiyarmu.”

Harin ya zo ne kwana guda bayan sojojin Syria sun ce sun daƙile wani harin jirage marasa matuka daga Iraki da aka kai kan al-Tanf, wani sansanin a kudu maso gabashin ƙasar da a baya ke dauke da dakarun Amurka.

Ƙungiyoyin Iraki masu goyon bayan Iran sun ɗauki alhakin hare-hare kan kadarorin Amurka a Iraki da sauran yankunan, yayin da su ma waɗannan ƙungiyoyin ke fuskantar hare-hare.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use