Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Peter Obi ya ce ya fi kowa cancantar shugabancin Najeriya

Peter Obi ya ce ya fi kowa cancantar shugabancin Najeriya Peter Obi ya ce ya fi kowa cancantar shugabancin Najeriya
Tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a LP Peter Obi (Hoto: FB/Peter Obi)

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi cancanta a cikin masu neman shugabancin ƙasa a halin yanzu.

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan rediyon Magic FM da ke Aba, inda ya zargi gwamnatin tarayya da cewa tana ƙoƙarin hana shi fitowa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Ya kuma ce hana shi shiga zaɓe mai zuwa na daga cikin manyan manufofin gwamnati mai ci.“Gwamnatin da ke mulki na ƙoƙarin ganin ban zama ɗan takara a kowace jam’iyya ba,” in ji shi.

Tsohon gwamnan jihar Anambrar ya ce matsalolin tattalin arziki da shugabanci da Najeriya ke fuskanta na buƙatar mutum mai ƙwarewa a harkokin kasuwanci da gudanarwa, yana mai bayyana kansa a matsayin wanda zai iya magance matsalolin ƙasar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use