Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Kwankwaso ya fice daga NNPP, ana sa ran komawarsa ADC

Kwankwaso ya fice daga NNPP, ana sa ran komawarsa ADC Kwankwaso ya fice daga NNPP, ana sa ran komawarsa ADC
Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Tsohon dan takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar NNPP.

Madugun darikar Kwankwasiyya ya ce ya bar jam’iyyar ce saboda a yanzu ya samu wata wacce zai shiga domin makomar siyasarsa a zaben 2027 da ke tafe.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yau Asabar jim kadan bayan komawarsa birnin Kano.

A yanzu ana sa ran Kwankwason zai koma jam‘iyyar adawa ta ADC a gobe Litinin kamar yadda wata sanarwa da kungiyar darikar Kwankwasiyya ta fitar a ranar Asabar, ta nuna.

Tsohon gwamnan na Kano ya ce a yanzu, ya zama dole a sama wa ‘yan kasa mafita.

A baya dai anyi ta rade-radin komawar tsohon gwamnan jam’iyyar ADC, tun bayan ganin fuskokin wasu jiga-jigan jam’iyyar a bikin Sallah da aka yi a jihar Kano wadanda suka hada da tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar Labour, Peter Obi da gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da kuma wasu kusoshin jam’iyyar NNPP.

A ranar Juma’ar da ta gabata ma an hangi Kwankwason da sakataren jam’iyyar ADC Ra’uf Aregbesola da kuma ziyarar da ya kai wa tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a Abuja.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use