Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da rusa Majalisar Zartarwar jihar nan take.
A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin bai wa duk wani jami’in gwamnati da ke da sha’awar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa damar yin hakan cikin sauƙi.
Gwamnan ya kuma umarci dukkan kwamishinoni da su mika ragamar ma’aikatunsu ga sakatarorin dindindin kafin ranar Juma’a, 3 ga Afrilu, 2026.
Zulum ya gode wa tsofaffin kwamishinonin bisa gudummawar da suka bayar, jajircewa da kuma irin ayyukan ci gaba da suka gudanar domin al’ummar jihar Borno.