An zaɓi Abdulrahman Mohammed a matsayin sabon shugaban jam’iyyar PDP, ɓangaren ministan Abuja, Nyesom Wike.
Sannan an kuma zaɓi Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa, a babban taron jam’iyyar na shekara ta 2026 wanda aka gudanar ranar Lahadi a Abuja, babban birnin Najeriya.
Mohammed da Anyanwu sun samu nasarar ce ta hanyar masalaha, tare wasu mambobin kwamitocin jam’iyyar na ƙasa 19.
Manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka halarci taron sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi da sauran mambobin jam’iyyar.
Haka kuma, an bayyana Nyesom Wike a matsayin jagoran jam’iyyar na ƙasa a taron da aka yi.
Ya ce jam’iyyar ta fara farfaɗowa daga matsalolin da ta shiga, kuma za a fafata da su a babban zaɓen Najeriya na 2027.