Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaban Najeria, Bola Tinubu, zai samu nasara mai yawa a yankin Arewacin Najeriya a zaɓe mai zuwa.
Sani ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya ce ana ci gaba da shirye-shirye musamman a jihar Kaduna domin tabbatar da cewa shugaban ƙasar ya samu kuri’u masu yawa a yankin.
Ya ƙara da cewa, duk da ƙalubalen da aka fuskanta a zaɓen da ya gabata, yanzu al’amura sun daidaita, yana mai nuna cewa shugabancin da Tinubu ya taimaka wajen haɗa kan al’umma tsakanin Arewa da Kudu.
A cewarsa, wannan haɗin kai zai ba Bola Ahmed Tinubu damar samun rinjaye mai yawa a Arewacin Najeriya.