Ministan jin kai da rage talauci, Yusuf Tanko Sununu, ya yi murabus daga mukaminsa domin mayar da hankali kan harkokin siyasa a jihar Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa Sununu ya ajiye aikinsa ne bisa ƙa’idojin ƙasar da ke buƙatar masu neman muƙaman siyasa su sauka daga mukaman gwamnati.
Ana rade-radin cewa tsohon Sununu na shirin tsayawa takarar sanatan Kebbi ta Kudu a zaɓen 2027.
Kafin murabus ɗin nasa, ya taɓa riƙe mukamai daban-daban a gwamnati, inda ake ganin ya bayar da gudunmawa ta fuskar ayyukan jin kai da ci gaban al’umma.