Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Trump ya yi barazanar fitar da Amurka daga NATO
Trump na shirin daukar mataki mai hadari da ‘zai zama bala’i ga Amurka ko Iran’
Tinubu ya nada sabon babban sakataren hukumar PTDF

Trump na shirin daukar mataki mai hadari da ‘zai zama bala’i ga Amurka ko Iran’

Trump na shirin daukar mataki mai hadari ga Amurka ko Iran Trump na shirin daukar mataki mai hadari ga Amurka ko Iran
Trump na shirin daukar mataki mai hadari ga Amurka ko Iran

Shugaban Amurka Donald Trump na shirin daukar wani gagarumin mataki mai sarkakiya da ka iya jefa Amurka ko kuma Iran cikin babbar matsala.

Tun bayan kaddamar da yakin da Washington tare da hadin gwiwar Isra’ila suka yi kan Iran, shugaba Trump ya fara tunanin tura sojin Amurka su shiga Tehran ta kasa domin cimma manufofinsa na yaki wadanda har yanzu masana ke cewa basu da alkibla.

Shin sojojin Amurka za su shiga Iran ta kasa? 

Zuwa tsakiyar shekarar 2025, tun kafin fara yaƙi da Iran, akwai sojojin Amurka tsakanin 40,000 zuwa 50,000 da aka jibge a yankin Gabas ta Tsakiya, waɗanda suka haɗa da waɗanda ke manyan sansanonin dindindin da kuma ƙananan wuraren aiki a yankin.

Tun farkon wannan shekarar, shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara adadin sojojin Amurka a yankin, inda aka fara tura jiragen ruwa na yaƙi, ciki har da jirgin ruwan daukar jiragen sama na USS Abraham Lincoln.

Bisa bayanan masana na open-source intelligence da kuma masu bibiyar bayanan jiragen sama na soja, Amurka ta tura jiragen sama sama da 120 zuwa yankin tun daga farkon watan Fabrairu. Wannan shi ne mafi yawan adadin sojojin sama na Amurka a Gabas ta Tsakiya tun bayan Yaƙin Iraki na 2003.

Rahotanni sun nuna cewa jiragen da aka tura sun haɗa da:

  • jiragen E-3 Sentry (AWACS) na sa ido da jagorancin yaƙi,
  • jiragen yaƙi na zamani F-35 masu ɓoye kansu,
  • jiragen F-22,
  • da kuma F-15 da F-16.

Bayanai sun nuna yawancin waɗannan jirage sun taso ne daga sansanonin Amurka da Turai, tare da goyon bayan jiragen ɗaukar kaya da na dakon mai, alamar cewa wannan wani shiri ne mai karfi na dogon lokaci, a cewar masana soja.

A ranar Talata, Ma’aikatar Tsaro ta Amurka Pentagon ta ba da umarnin ƙara tura wasu sojojin Amurka zuwa yankin Tekun Fasha.

Ƙarin sojojin da aka tura sun kasu kashi uku:

Na farko akwai rukunin Tripoli Amphibious Ready Group, wanda ya ƙunshi jirgin yaƙi na USS Tripoli da rundunar sojin ruwa ta 31st Marine Expeditionary Unit (MEU).

Na biyu shi ne rukunin Boxer Amphibious Ready Group, wanda ya kunshi jirgin USS Boxer da rundunar MEU ta 11, daga Kudancin California a Amurka.

Wadannan rundunoni biyu na sojin ruwa sun sa adadin sojin Ruwan Amurka ya kai kusan 4,500 a yankin.

Na uku kuma ita ce runduna mai kusan sojoji 2,000 daga rundunar sojin sama ta 82 ta Airborne Division, wadda ke da hedikwata a Fort Bragg, a arewacin Carolina. Wannan runduna ta ƙware wajen hari ta sama.

Gaba ɗaya, kusan sojoji 7,000 ne Amurka ta ƙara tura su tun bayan kaddamar da yaki kan Iran.

Jiragen sojin Amurka a kan babban jirgin yakin kasar na Abraham Lincoln (Hoto: NSCBC)

Shin wannan adadin zai iya isa a yi mamaya ta kasa?

Har yanzu Amurka ba ta sanar da wani shiri na mamaya ta ƙasaba a Iran ba.

Sai dai rahotannin kafafen yaɗa labarai na Amurka sun nuna cewa Pentagon na duba yiwuwar ƙara tura sojoji 10,000 a ƙasa, baya ga waɗanda aka riga aka tura.

Idan ta tabbata, hakan na nufin Amurka za ta samar da kusan sojoji 17,000 a ƙasa a Iran.

Har yanzu ba a san ko wasu ƙasashe za su tura sojojinsu don yaki da Amurka ko kuma a a ba.

Duk da haka, wannan adadi bai kai yawan sojojin da Amurka ta tura a baya ba, idan aka kwatanta da lokacin da ta kai hari Iraki a shekarar 2003.

A lokacin, Amurka ta shiga Iraki ne a ranar 20 ga watan Maris din 2003 da sojoji 150,000, tare da ƙarin wasu 23,000 daga wasu ƙasashe.

A shekarar 2011, watanni shida kafin janye sojojin Amurka gaba ɗaya daga Iraki, akwai kusan sojojin Amurka 45,000 a ƙasar wadanda suka tsaya domin horarwa da ba da shawara ga sojojin Iraki.

Zuwa tsakiyar 2025 kuwa, akwai kusan sojojin Amurka 2,500 da suka rage a Iraki, amma daga baya an mayar da yawancinsu zuwa wasu ƙasashe kamar su Siriya da sauransu.

Majiya: Al Jazeera, WSJ, Explorer Hausa

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use