Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

An tsinci gawar jigo na APC Kano a elebeto wani otel a Abuja

An tsinci gawar Skataren tsare-tsare na APC a jihar Kano Abdulsalami Ginsau a wani otel a Abuja An tsinci gawar Skataren tsare-tsare na APC a jihar Kano Abdulsalami Ginsau a wani otel a Abuja
An tsinci gawar jigo a APC Kano a wani otel a Abuja

An tsinci gawar mataimakin sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC reshen jihar Kano, Abdulsalami Ginsau, a elebeto wani otel a Abuja da ke yankin Utako a babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin yana daga cikin waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen shirya wani taron jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa Ginsau ya rasu ne sakamakon makalewa a wata na’ura ta otel ɗin.

Haka kuma, bincike ya nuna cewa Abdulsalami Ginsau ya rasu tun ranar 27 ga watan Maris da ya gabata.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use