Jam’iyyar ADC a Najeriya ta tabbatar da kudurinta na ci gaba da gudanar da dukkanin zaɓukan cikin gida daga matakin gunduma har zuwa matakin ƙasa, duk da ce-ce-ku-ce da ke tattare da lamarin.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa sa ido da INEC ke yi a irin waɗannan zaɓuka ba wajibi ba ne.
Ya kuma jaddada cewa umarnin kotu bai cire kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) da David Mark ke jagoranta ba.
Abdullahi ya ƙara da cewa tuni jam’iyyar ta sanar da INEC kan shirinta na gudanar da zaɓukan, kuma hukumar ta karɓa tare da tabbatar da samun sanarwar a hukumance.