Shugaban hukumar zaɓe ta kasa INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bukaci jam’iyyar ADC da ta dakatar da shirinta na gudanar da babban taron ƙasa domin kauce wa matsalolin doka.
Ya ce wannan gargadi ya zama dole ne domin kada a maimaita irin kura-kuran da suka faru a jihohin Zamfara da Filato, inda rikice-rikicen cikin gida suka jawo matsala a harkokin zaɓe.
INEC ta bayyana cewa har yanzu akwai shari’a a kotu kan rikicin shugabanci a ADC, don haka duk wani mataki da ya saba wa umarnin kotu na iya haifar da matsala ga jam’iyyar.
Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin cikin gida ke ci gaba da tsananta a ADC, gabanin zaɓen shekarar 2027.