Rahotanni daga ƙasar Iran sun bayyana cewa jami’an tsaron ƙasar sun harbo wani jirgin yaƙin Amurka, lamarin da ya ƙara tsananta tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu.
Wani jami’in Amurka ya tabbatar wa Reuters cewa an tura jirgin ne domin gudanar da bincike kan wasu muhimman wurare a babban birnin Iran, tare da yiwuwar kai farmaki.
Lamarin na zuwa ne bayan rahotanni cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kai hari kan wata gada mai muhimmanci a yankin Karaj, kusa da babban birnin Iran.
Haka kuma, Trump ya yi barazanar kai wasu sabbin hare-hare kan tashoshin makamashi da sauran manyan kadarorin ƙasar.
A nasa ɓangaren, Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa waɗannan barazanar na Trump yunƙuri ne kawai na janyo babban rikici, kuma suna barazana ga zaman lafiya a yankin.