Amurka da Isra’ila sun kai hari kan tashar makamashin nukiliya ta Bushehr a Iran, inda rahotanni suka ce harin ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da lalata wasu sassan wurin.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa yana iya janyo babbar barazana ga yankin baki ɗaya.
Ya ce fitar tururin makamashin nukiliya sakamakon irin wannan hari na iya haddasa asarar rayuka a manyan biranen ƙasashen Gulf (GCC), ba wai a Tehran kaɗai ba.
Araghchi ya kuma yi tuni kan yadda ƙasashen Yamma suka nuna damuwa kan rikice-rikicen da suka shafi tashar nukiliyar Zaporizhzhia a Ukraine, yana mai cewa ya kamata a yi la’akari da irin wannan haɗari a Iran ma.
Haka kuma, ya ƙara da cewa hare-haren da ake kai wa kan cibiyoyin sinadarai na Iran na nuna ainihin manufar waɗanda ke kai harin, yana mai jaddada cewa ƙasarsa za ta ci gaba da kare kanta.