Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, kuma jigo a jam’iyyar ADC, ya ce, ya shirya tsaf don mara wa duk wanda ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Kazalika, Atiku ya ce, batutuwan da ake yadawa na cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na iya dankwafar da jam’iyyar a zabukan 2027ba za su kai ko inaba.
Atiku ya bayyana haka ne yayin wata hira da DW Hausa a ranar Asabar.
Ya jaddada cewa lalata jam’iyyar ba zai yiwu ba, sakamakon karbuwar da ADC ta ke ci gaba da samu a tsakanin al’ummar Najeriya.