Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana damuwarsa kan yadda Kiristoci ke fuskantar gallazawa a Najeriya da wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya, ciki har da Siriya, Lebanon da Turkiyya.
A cikin sakon taya murnar bikin Easter da ya yi wa Kiristoci a duniya, Netanyahu ya ce Isra’ila ce kadai ke kare ‘yancin Kiristoci a cikin yankin, inda ya bayyana cewa al’ummar Kiristoci a ƙasar suna ƙaruwa kuma suna samun ci gaba.
Ya jaddada cewa ko a lokacin hare-haren makamai masu linzami, Isra’ila da Amurka na tsayawa tsayin daka kan Iran da gungun ‘yan ta’addarta, tare da tabbatar da kare ‘yancin addini ga kowane mai bi, musamman a wannan lokaci mai tsarki.