Shugaban Donald Trump na Amurka ya ce sojojin ƙasar sun ceto matuƙin jirgin yaƙin ƙasar da ya ɓace a kudancin Iran, bayan harbo jirginsa a ranar Juma’a.
Wata sanarwa da Mista Trump ya wallafa a kafofin sada zumunta, ya ce sojojin sun gudanar da aikin ceto mafi jarumta a tarihin Amurka.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi mummunan artabu tsakanin sojin Amurka da kuma na Iran a lokacin aikin.
Hotunan bidiyo da aka wallafa a kafofin sada zumunta sun nuna yadda ɗaruruwan mutane ke tururuwar zuwa yankin mai tsaunuka a kudu maso yammacin Iran don taimakawa wajen gano inda sojan yake.