Iran ta yi watsi da wa’adin da sa’a 48 da shugaban Amurka Donald Trump ya sanya mata cewa a cimma yarjejeniya ko a buɗe mashigar Hormuz.
Wata sanarwa da shugaban rundunar ƙoli ta sojin Iran, Janar Ali Abdollahi ya fitar, ya kwatanta Trump a matsayin mutum mai wauta.
Ya yi gargaɗin cewa abin da Trump ke fatan saukar wa Iran zai kare kan Amurka.
“Idan Amurka ta kai hari kan muhimman kayayyakin more rayuwa na Iran, to Tehran za ta kai hari kan wuraren da sojojin Amurka da Isra’ila,” in ji shi.