Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Ana neman mutum 70 bayan kifewar kwale-kwalen ‘yan ci-rani a tekun Libya

Ƴan ci-rani Ƴan ci-rani
Ɗaruruwan ‘yan ci-rani ne ke mutuwa duk shekara yayin tsallakawa zuwa Turai (AFP via Getty Images)

Sama da mutum 70 ne suka bata bayan da wani jirgin ‘yan ci-rani ɗauke da mutum 105 ya kife a tekun Libya.

Cikin mutanen da jirgin ya kife da su har da yara.

Sai dai, an samu nasarar ceto mutum 32 da kuma gawawwaki biyu, a cewar wata kungiyar ceto a teku.

Ɗaruruwan ‘yan ci-rani ne da ke tsallakawa zuwa Turai don samun rayuwa mai inganci ke mutuwa a kowace shekara a cikin teku.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use