Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Ƴan Najeriya za su ji daɗi nan gaba kaɗan – Shettima

Kashim Shettima Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya tabbatarwa ƴan ƙasae cewa za su ji daɗi nan gaba kaɗan saboda irin manufofin da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke tsarawa karkashin shirin Renewed Hope.

Shettima ya bayyana haka ne a sakonsa na murnar bikin Easter ga ƴan Najeriya, inda ya ce ƙasar za ta shawo kan matsalolin tattalin arziki da kuma na tsaro da take fama da su.

“Lokacin Easter na tuna mana cewa duk waɗanda suke yin fata mai kyau nasara na tare da su. Lokaci na yin fata kan raɗaɗi da kuma imani da ke rinjayar fargaba,” in ji Shettima.

Ya ce gwamnati na iyakar kokari wajen tabbatar da zaman lafiya, farfaɗo da tattalin arziki da kuma cigaba mai ɗorewa, inda ya ce duk wani cigaba na buƙatar sadaukarwa.

“Ina da yakinin cewa tare da haɗin kai, sadaukarwa da kuma imani, za mu fita daga cikin kowane irin matsala muke ciki a ƙasar nan,” in ji mataimakin shugaban ƙasar.

Ya kuma buƙaci ƴan ƙasar da su guji duk abin da zai raba kawunansu, tare da rungumar ɗabi’u na zama al’umma ɗaya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use