Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

NDLEA ta kama wani fasto da matarsa ɗauke da tabar wiwi a Lagos

NDLEA NDLEA
NDLEA ta ce an kama wiwi ɗin ɓoye cikin wasu abubuwa da aka lullube (NDLEA/X)

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDELA, sun cafke wani fasto da matarsa ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilogram 11 a cikin motarsu, a kan iyakar Seme da ke jihar Lagos.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya fitar, ya ce an kama faston ne mai suna Afolabi Hodonu mai shekara 45 da ya kasance shugaban cocin Celestial Church of Christ da ke yankin Badagry, da kuma matarsa Success mai  shekara 35 – ranar 2 ga Afrilu yayin da suke tafiya a cikin motarsu ƙirar Honda Pilot SUV a iyakar Seme.

Babafemi ya ce binciken da aka yi wa motar ce ya sa aka gano tabar wiwi ɗin ɓoye cikin wasu abubuwa da aka lulluɓe ta.

Ya ce kamen ya zo ne bayan samun bayanan sirri daga wurin wani da ake zargi mai suna Sunday Samuel ɗan shekara 35, wanda aka kama yana ayyana kansa a matsayin jami’in tsaro.

An kama shi ne ranar 30 ga watan Maris a shingen binciken da aka kama faston, yana ɗauke da wiwi mai nauyin kilogram 24.5.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use