Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

MURIC ta bukaci Amupitan ya sauka daga mukaminsa

MURIC ta bukaci Amupitan ya sauka daga mukaminsa MURIC ta bukaci Amupitan ya sauka daga mukaminsa
Farfesa Ishaq Akintola, Shugaban Ƙungiyar MURIC

Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta bukaci a sauke shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, tare da ayyana shi a matsayin wanda ba a bukata.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar ta zargi Amupitan da gaza wa wajen tafiyar da ayyukansa yadda ya kamata, tare da cewa hakan na iya kawo matsala ga tsarin dimokuraɗiyya.

MURIC ta kuma bayyana cewa dole ne ya sauka daga mukaminsa domin tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin zabe a Najeriya.

Kungiyar ta jaddada cewa matakin da ta dauka ya zama dole domin kare muradun jama’a da kuma inganta tsarin zabe a kasar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use