Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Masu gidajen Rediyo da Talabijin sun bukaci Wike ya janye kalaman barazana da ya yi

Masu gidajen Rediyo da Talabijin sun bukaci Wike ya janye kalaman barazana da ya yi Masu gidajen Rediyo da Talabijin sun bukaci Wike ya janye kalaman barazana da ya yi
Nyesom Wike, Ministan babban birnin tarayya Abuja

Ƙungiyar masu gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu a Najeriya (IBAN) ta bukaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da ya janye kalamansa tare da ba da hakuri, da kuma barazanar kaurace wa duk wata hulɗa da shi a kafafen yaɗa labarai.

Wannan na zuwa ne bayan kalaman da Wike ya yi a wani taron manema labarai, inda ya mayar da martani ga ɗan jarida Seun Okinbaloye, har ya furta cewa da zai samu dama “zai harbe shi.”

Ƙungiyar IBAN ta bayyana wannan furuci a matsayin abin da bai dace ba, tana mai cewa yana iya zama barazana ga ‘yan jarida da kuma ‘yancin faɗar albarkacin baki.

Duk da cewa an ce Wike ya yi bayanin cewa ba hakan yake nufi ba, ƙungiyar ta jaddada cewa irin wannan magana daga manyan jami’an gwamnati na iya tsoratar da kafafen yaɗa labarai.

IBAN ta yi kira gare shi da ya ba da hakuri ga ɗan jaridar da kuma kafafen yaɗa labarai, tare da gargaɗin cewa idan bai yi hakan ba, za su iya kaurace wa duk wani taron manema labarai da hulɗa da shi a Najeriya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use